in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin shugaba Xi Jinping na kasar Sin don murnar sabuwar shekarar ta 2018
2017-12-31 19:00:07 cri

Abokan aiki da abokan arziki, maza da mata: 

Shekarar 2018 shekara ce ta farko wajen aiwatar da manufofin da aka tsara a yayin babban taron wakilan JKS karo na 19 daga dukkan fannoni. A yayin wannan muhimmin taro, an tsara babbar manufar raya kasarmu nan da shekaru 30 masu zuwa. Idan ana son gina wani gini mai tsayi, dole ne a kafa tushensa mai inganci. Idan muna fatan mayar da manufar da ta zama abin gaskiya, dole ne mu gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata, a maimakon yin mafarki ko kuma tsara shiri kawai.

A shekarar 2018, za a cika shekaru 40 da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje. Manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, manufa ce da dole ne kasar Sin take bi domin samun ci gaba da cimma burin kasar. Za mu yi amfani da zarafin yin murnar cika shekaru 40 da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, wajen warware matsalolin da muke fuskanta, zamu zurfafa gyare-gyaren da muke yi kamar yadda ya kamata.

Ya zuwa shekarar 2020, za mu kubutar da dukkan masu fama da talauci daga kangin talauci bisa ma'aunin da muke bi yanzu, wanda shine alkawarin da muka dauka a tsanake. Yanzu ya rage shekaru 3 kawai. Dole ne dukkan al'ummar kasar su dauki matakan da ake bukata bisa hakikanin halin da ake ciki, ta yadda za a iya rika samun sabbin nasarori kamar yadda ake fata. Samun nasarar kawar da talauci gaba daya cikin lokaci bayan shekaru 3, shine karo na farko da za a fitar da dukkan al'ummar Sin daga kangin talauci a tarihin Sin cikin dubban shekarun da suka gabata. Bari mu hada kanmu wajen kammala wannan babban aiki, wanda yake da matukar muhimmanci ga al'ummar Sin dama dukkan 'yan Adam baki daya.

1  2  3  4  5  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China