Takardar da sama da kungiyoyi 10 suka gabatarwa hukumar UNESCO daga kasar Sin,Koriya ta kudu da wasu kasashe da yankuna game da wadannan mata, zai nunawa duniya irin yadda aka gallaza musu a lokacin yaki, kana a tuna da tarihi, a kuma rungumi zaman lafiya da kare martabar dan-Adam, kamar yadda ya shaidawa taron maname labarai.
Ya ce hakkin kungiyoyin kasa da kasa ne su biya kudadensu na zama mamba a kan lokaci. Kasar Sin ta bukaci Japan da ta waiwayi barnar da ta aikata a baya, kana ta gyara kura-kuranta sannan ta daina wani kauce-kauce game da wannan takarda.
Mr. Lu Kang ya ce yadda aka rika sanya wadannan mata cikin wannan yanayi da karfi ko tilasta musu yin lalata,wani mummunan laifi da sojojin Japan suka aikata a lokacin yakin duniya na biyu. Kuma akwai kwararan shaidu dake tabbatar da hakan.(Ibrahim)