Kasar Sin na son tallafawa kasar Philippines da mahaukaciyar guguwa ta shafa
Madam Hua Chunying, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta furta a yau Talata cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon jaje ga takwaransa na kasar Philippines Rodrigo Duterte, sakamakon mahaukaciyar guguwar nan mai lakabin "TEMBIN" da ta aukawa kasar ta Philippines, wadda ta haddasa asarar rayuka da dukiyoyi da dama. A cewar Madam Hua, kasar Sin tana son baiwa kasar Philippines tallafin ceton jama'arta.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku