in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Jamhuriyar Congo ta kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta da 'yan adawa
2017-12-24 12:32:13 cri
Gwamnatin Jamhuriyar Congo ta kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta da dakarun kungiyar adawa mai taken "Ninja" dake lardin Pool na kasar a jiya Asabar, inda bangarorin 2 suka tsai da niyyar kafa wani kwamiti mai kunshe da mambobi na bangarori daban daban, wanda zai sa ido kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla. An sanar da haka ne a wajen taron manema labaru da bangarorin gwamnatin Jamhuriyar Congo da 'yan adawa suka kira a birnin Brazaville, fadar mulkin kasar, a jiya. Bisa wannan yarjejeniyar tsagaita bude wutar, an bukaci dakarun kungiyar "Ninja" da su kwance damarar yaki, da daina ayyukan da ka iya hana ruwa gudu a kokarin maido da tsaro da zaman lafiya a kasar. Sa'an nan a bangaren gwamnati, ta yi alkawarin dawo da mambobin kungiyar adawar cikin al'ummar kasar, bayan da suka gama aikin mika dukkan makaman da suka mallaka ga gwamnati. Haka zalika, an kayyade cikin yarjejeniyar cewa, za a kula da jama'ar lardin Pool, wadanda suka rasa muhallansu a sanadiyyar yakin, da kuma 'yan gudun hijira dake sauran wurare. Dama dai sakamakon rikice-rikicen da dakaru masu adawa da gwamnati suka tayar a lardin Pool, fararen hula da yawa sun rasa muhallansu. Ban da haka kuma, yayin da aka gudanar da zabukan majalisar dokoki da kananan hukumomin kasar a watan Yulin bana, an kasa gudanar da zabe a lardin Pool saboda rashin kwanciyar hankali a yankin.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China