in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta inganta musaya tsakanin al'ummominta da na kasashen waje
2017-12-22 10:28:18 cri

Hukumomin tsakiya na kasar Sin sun yi kira da a inganta musayar ra'ayoyi tsakanin al'ummomin kasar da na kasashen waje.

A cewar wani shiri da daukacin ofisoshin kwamitin tsakiya na JKS da kuma majalisar gudanawar kasar suka fitar, musayar ra'ayi tsakanin jama'a na kara karfafa fahimta a tsakaninsu.

Shirin ya kuma bukaci inganta harkokin diflomasiyya tsakanin shugabannin kasashe da manyan tarukan diflomasiyya da musaya tsakanin al'ummu domin jan hankalin karin kasashe su shiga a dama da su a shirin musayar.

Ya nuna cewa, ya kamata musaya tsakanin jama'a ya kara fadada da armashi, sannan kasar ta mara baya ga shirye-shiryen musaya kan al'adu masu karfi da suka hada da harshen Sinanci da magungunan gargajiya na Sinawa da fasahohin kokawa da bukukuwan gargajiya.

Shirin ya kuma yi alkawarin musayar dabarun kasar Sin a bangaren rage talauci da samar da ilimi da kiwon lafiya da kasashen waje, da kara kaimi wajen tallafawa kasashe masu tasowa.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China