in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kara yin hadin gwiwa a ilimin kasa da kasa
2017-12-19 09:31:43 cri
Ma'aikatar ilimi ta kasar Sin ta bayyana a jiya Litinin cewa, ya zuwa karshen shekarar 2016, Kasar ta kulla yarjejeniya da wasu kasashe da yankuna 47 domin amincewa da takardun karatun difloma da na digiri na kasashen juna.

Bugu da kari, kasar ta Sin ta gabatar da wasu manyan shirye-shiryen guda 8 a fannonin al'adu da musaya tsakanin jama'a, da kasashen da suka hada da Rasha da Amurka da Burtaniya da Faransa, Sauran sun hada da Jamus da Indonesiya da kuma Afirka ta kudu.

Haka kuma ya zuwa karshen shekarar 2016, ma'aikatar Ilimi ta kasar ta Sin ta amince da hukumomi da shirye-shiryen koyar da Ilimi kimanin 2,500 da aka bude tsakanin Sin da kasashen waje.

Ma'aikatar ta kara da cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata kasar Sin ta kulla hadin gwiwa a fannin Ilimi da musaya da kassashe da yankuna 188. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China