in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe zai nada mataimakansa nan ba da jimawa ba
2017-12-16 12:41:28 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya ce zai nada mataimakansa biyu cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Emmerson Mnangagwa, ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabin rufe taron yini guda da jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar ta yi jiya a birnin Harare, inda ta amince da shi a matsayin shugabanta, kuma dan takararta na shugaban kasa a badi.

A ranar 24 ga watan Nuwamban da ya gabata ne Emmerson Mnangagwa ya karbi mulkin kasar, biyo bayan tilastawa tsohon shugaban kasar Robert Mugabe yin murabus da sojoji suka yi, bayan ya shafe shekaru 37 yana rike da ragamar mulkin kasar.

Tuni dai sabon shugaban ya nada ministocinsa, abun da ya rage kawai yanzu shi ne nada mataimakansa biyu.

Sabon shugaban kasar ya kuma godewa jam'iyyar ZANU-PF bisa zabarsa da ta yi a matsyain shugabanta, inda ya lashi takobin yin aiki tare da dukkan mambobinta don farfado da tattalin arzikin kasar da samar da aikin yi ga al'umma. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China