in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimbabwe ya sha alwashi murkushe cin hanci da rashawa
2017-12-15 13:50:03 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya sha alwashin sanya kafar wando daya da masu aikata cin hanci da rashawa, da masu rub da ciki kan dukiyar gwamnati, muddin ba su maido da abun da suka wawura ba.

Da yake gabatar da jawabin farko ga mambobin kwamitin koli na jam'iyyar sa ta Zanu-PF a jiya Alhamis, Mr. Mnangagwa ya baiwa wadanda suka san sun kwashi dukiyar kasar wa'adin watanni 3 su mayar ko kuma su fuskanci fushin gwamnatin sa.

Mr. Mnangagwa ya ce ya zama wajibi gwamnatin sa ta yaki cin hanci da rashawa, tare da samar da guraben ayyukan yi ga al'ummar ta.

"Ina da sunayen masu safarar kudin kasa zuwa ketare. A watan Maris mai zuwa bayan cikar wa'adin watannin nan 3, wadanda ba su ji bari ba, ko shakka babu zan kira sunayen su na kunyata su", a kalaman shugaba Mnangagwa.

Shugaban ya ce jam'iyyar dake mulki na bukatar sauya tunani, ta yadda za ta kara mai da hankali ga bunkasa tattalin arzikin kasa, maimakon dukufa fannin siyasa kadai.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China