Tarihin wasan
An ce cikin al'ummomin duniya, mutanen kabilar Inuit dake zama a arewacin nahiyar Amurka ne suka fara gudanar da wasan trampolining. Mutanen Inuit, yayin da suke gudanar da wani biki na murnar kamun kifaye da yawa, su kan sanya mutane suka yi da'ira, suka rike wata fatar dabba yayin da wani mutum ya tsaya a kai. Sa'an nan mutanen za su janye fatar domin daga mutumin, har ya shiga sama. Daga baya za su dinga daga shi zuwa sama a kai a kai. Ka ga hakan ya yi tamkar wani tsohon salon wasan trampolining.
Gasanni iri-iri da ake gudanar da su da Trampoline
Ban da gasar da ake gudanar tsakanin daidaikon 'yan wasa, akwai kuma gasar da ake yi tsakanin 'yan wasa biyu-biyu, inda ake sanya 'yan wasa 2 na kungiya guda su yi tsalle kan na'urorin Trampoline 2 da suka kasance a dab da juna. Sa'an nan ana bukatar 'yan wasan 2 da su yi motsi irin daya. Idan motsinsu ba iri daya ba, ga misali idan wani ya yi sauri, yayin da wani na daban saurinsa bai kai na waccan ba. To, za a rage musu maki.
Ban da wannan kuma, akwai gasar Double Mini-Trampoline ko kuma DMT. Gasar ta bukaci 'yan wasa su nuna fasahohinsu kan wata doguwar na'urar Trampoline, inda za su yi gudu, sa'an nan su yi tsalle su hau na'urar, wadda za ta daga su sama, inda za su nuna wasu motsi na musamman kafin su sake tsalle karo 2-3 tare da nuna wasu motsi na daban.(Bello Wang)
171123-wasan-trampolining-mai-nishadantarwa-bello.m4a
|