Tashar jirgin kasan ta kudancin Zhangjiakou tana lardin Hebei, zata dinga kammala aikinta ne a daren ranar Asabar bayan jirgin kasar na fasinja ya kammala jigilarsa. Daga nan sai ya canza zuwa tashar Shalingzi dake yammacin birnin.
Tashar ta kudancin Zhangjiakou ta gudanar da aikin jigilar fasinjoji sama da miliyan 20, tun daga lokacin data fara aiki a shekarar 1957. Tashar ba zata iya biyan muradun yawan fasinjojin dake karuwa a yankin a kullum ba.
Ana saran za'a kammala aikin layin jirgin kasan mai saurin tafiya mai nisan kilomita 174 daga Beijing zuwa Zhangjiakou nan da shekarar 2019, inda za'a rage tsawon lokacin da ake shafewa wajen zirga zirgar tsakanin biranen biyu daga awowi uku zuwa mintoci 50.(Ahmad Fagam)