in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WADA ta ci gaba da dakatar da aikin hukumar yaki da maganin kara kuzari ta kasar Rasha
2017-11-29 09:50:44 cri
Hukumar yaki da shan maganin kara kuzari ta duniya wato WADA, ta tsaida kuduri a kwanakin baya, na ci gaba da dakatar da aikin hukumar yaki da amfani da maganin kara kuzari ta kasar Rasha.

A gun taron majalisar hukumar WADA da aka gudanar a birnin Seoul dake kasar Koriya ta Kudu, an tsaida kuduri cewa, bai kamata a mayar da izinin aikin hukumar yaki da maganin kara kuzari ta kasar Rasha ba.

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Rasha Alexander Zhukov ya bayyana cewa, kasarta ta amince hukumar yaki da amfani da maganin kara kuzarin ta su ba ta gudanar da aikin ta yadda ya kamata ba, amma babu wani tsari na goyon bayan amfani da maganin kara kuzarin da kasar ta aiwatar.

A gun taron kwamitin wasannin Olympics ta duniya da za a gudanar da watan Disamba, za a tattauna ko a amince da kasar Rasha ta halarci gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi ta Pyeong Chang ko a'a.

A karshen shekarar 2015, majalisar WADA ta zartas da daftarin hukumar yaki da amfani da maganin kara kuzari ta kasar Rasha, cewa hukumar ba ta bi ka'idojin WADA ba, kana ta sanar da dakatar da aikin wannan hukuma. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China