Mr. Mnangagwa, wanda ya kasance shugaban kasar ta Zimbabwe na biyu a tarihin ta, ya maye gurbin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe a watan Nuwamba, zai kuma yi takarar shugabancin kasar na shekarar 2018, kasa da shekara guda da karbe ikon kasar.
Ana sa ran wakilan jam'iyyar ta Zanu-PF kimanin 6,000 ne za su halarci taron, wanda zai gudana a birnin Harare, inda za a tabbatarwa shugaban mai ci mukamin babban sakataren jam'iyyar.
Tun a taron kwamitin tsakiyar jam'iyyar na watan Nuwamba ne dai aka tabbatarwa Mr. Mnangagwa damar takarar shugabancin kasar, karkashin jam'iyyar ta Zanu-PF mai mulkin kasar.