in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin Sulhu na MDD ta tantance batun Palasdinu
2017-12-09 12:44:07 cri
Kwamitin Sulhu na MDD ya gudanar da wani taro kan batun yankin gabas ta tsakiya a jiya Jumma'a, inda mahalarta taron suka fi mai da hankali kan batun Palasdinu.

Da yake tsokaci game da lamarin, wakilin kasar Sin dake jagorantar tawagar kasar a MDD Wu Haitao, ya furta a wajen taron cewa, kasar Sin na fatan bangarori masu ruwa da tsaki a wannan batu, za su dora muhimmanci kwarai kan yanayin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, tare da magance daukar matakan da ka iya tsananta rikici.

A cewar wakilin kasar ta Sin, lamarin matsayin birnin Kudus yana janyo hankalin kasar Sin. A ganin sa, kwamitin sulhu na MDD ya riga ya zartas da kudurori daban daban, wadanda suka kayyade matsayin birnin. Saboda haka, duk wani yunkurin radin kai, na neman canza matsayin birnin zai girgiza tushen da ake bi wajen daidaita batun Palasdinu, ya kuma ta da sabon rikici a yankin gabas ta tsakiya.

Kasar Sin, in ji mista Wu, tana tsayawa tsayin daka kan yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, da goyon bayan Palasdinawa, a kokarinsu na dawo da hakkinsu na halal, wato kafa kasar Palasdinu mai cikakken 'yancin kai, wadda ke mallakar gabashin birnin Kudus a matsayin hedkwatarta.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China