De Mistura ya ce, gwamnatin Syriar ta sanar da shi a jiya Alhamis cewa, tawagar za ta dawo birnin Geneve don shiga a dama da ita a tattaunawar, a kokarin da ake na samar da zaman lafiya, bayan da kasar ta shafe shekaru bakwai tana fama da mummunan tashi hankali.
Jami'in na MDD ya kuma shaidawa manema labarai a ofishin MDD dake Geneva cewa, ana ci gaba da tattaunwa da bangaren 'yan adawa, game da rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar da kuma zabukan da za a gudanar a kasar karkashin kulawar MDD, dukkan su ba tare da gindaya wasu sharudda ba.
A ranar 28 ga watan Nuwamba ne dai aka fara sabon zagayen tattaunawar zaman lafiyar Syriar da MDD ke jagoranta. Za kuma a ci gaba da gudanar da taron har zuwa ranar 15 ga watan Disamba a birnin Geneva.(Ibrahim)