Cikin sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta shafin ta na yanar gizo, ta ce ana sa ran wakilai mahalarta taron za su tsara wani shiri, na samar da reshen da zai lura da sakin wadanda ake tsare da su, da mika gawawwakin wadanda suka rasu, tare da fara binciken wadanda suka bace.
Har ila yau yayin taron, za a tattuna game da hanyoyin dakile tashe tashen hankula a wasu sassan kasar ta Syria, tare da amincewa da sanawar da ta shafi bukatun jin kai a yankunan kasar da yaki ya daidaita.
Wannan taro dai na zuwa ne bayan wata ziyarar ba zata da shugaban Rasha Vladimir Putin ya kai kasar ta Syria a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa kasar sa, na daf da kwashe dakarun sojin ta daga Syria, bayan da aka cimma nasarar murkushe 'yan ta'adda a cikin kasar.