in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin C919 na kasar Sin na biyu ya kammala gwajin tashi cikin nasara
2017-12-18 09:07:16 cri

A jiya ne jirgin saman fasinja na biyu samfurin C919 da kasar Sin ta kera ya gudanar da tashin gwaji cikin nasara, matakin da ke shirin sanya kasar Sin zama kasar dake kan gaba a fannin kera jiragen sama.

Jirgin na C919 dai ya tashi ne daga filin jiragen sama na kasa da kasa na Pudong dake Shanghai da misalin karfe 10 da rabi da safe, agogon kasar Sin, inda ya shafe kusan sa'o'i biyu yana shawagi a sararin samaniya. A lokacin da yake sararin samaniya, jirgin ya jarraba manyan tsare-tsare da na'urorinsa, kamar yanayin tashi da sauka, sadarwa, da yadda yake tafiya a sararin samaniya, yanayin gudu da sauransu.

Idan ba a manta ba a cikin watan Mayun wannan shekara ce, kasar Sin ta kera jirgin C919 na farko. Kana ya kammala gwajin tashi daga wani birni zuwa wani a watan Nuwamba.

Kamfanin kera jiragen saman fasinja na kasar Sin, yana shirin kera jiragen sama guda shida wadanda za a rika yin gwaji da su. Ana kuma sa ran za a gudanar da tashin gwaji sama da 1,000.

Jirgin na C919 wanda ke iya tafiyar kilomita 4,075, zai kuma iya yin gogayya da jirgin Airbus 320 da sabon jirgin kamfanin Boeing 737. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China