Kamfanin kera jiragen saman fasinja na kasar Sin (COMAC) ta bayyana a yau Laraba cewa, an tsayar da ranar 5 ga watan Mayun wannan shekara don kaddamar da tashin jirgin saman fasinja na farko kirar C919 da kasar Sin ta kera.
Yanzu haka dai masu sha'awar sayen jirgin daga ciki da wajen kasar Sin 23 ne suka gabatarwa kmfanin na COMAC oda kimanin 570, ciki har da kamfanin zirga-zirgar jiragen saman kasar Sin na Air China da kamfanin kula da zirga-zirgar jiragen sama na GE.
Shi dai wannan jirgin saman fasinja yana iya daukar fasinjoji 158 kuma zai iya cin zangon da ya kai kilomita 4,075. (Ibrahim Yaya)