An ba da odar sayen sabon jirgin sama samfuri C919 mallakar kasar Sin, kawo yanzu adadin bukatar sayen jiragen ya kai 730, bayan da wasu 'yan kasuwa 4 suka kulla yarjejeniyar sayen jiragen tare da kamfanin kera jirgin.
Hukumar kula da hada hadar jiragen sama ta kasar Sin COMAC, da kamfanin kera jiragen sama na C919 wanda ke da sansaninsa a birnin Shanghai, sun kulla yarjejeniyar cinikin jiragen da wasu kananan kamfanoni 4 a lokacin bikin baje kolin jiragen sama na Beijing Aviation Expo wanda aka bude a ranar Talata.
Jirgin saman wanda ke cin nisan zangon kilomita 4,075, C919 zai iya gogayya da Airbus 320 da sabon samfurin jiragen sama na Boeing 737.(Ahmad Fagam)