in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bukaci daukar matakan kariya yayin gwajin jirgin sama kirar kasar Sin
2015-11-02 18:50:31 cri
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bukaci sassan da abun ya shafa, da su dauki managartan matakai domin cimma nasarar gwajin jirgin saman nan mai lamba C919 kirar kasar Sin.

A sakon sa na taya murna ga kammalar kirar wannan jirgin fasinja, shugaba Xi ya bayyana bukatar daukar matakan kare hadurra, tare da tabbatar da ingancin jirgin sama da komai.

Kamfanin hada-hadar sufurin jiragen sama na COMAC ne dai ya kera wannan jirgi. Da zarar kuma an fidda shi kasuwa, jirgin zai yi takara da jirage na zamani, kamar su Airbus 320 da kuma Boeing 737.

A shekara mai zuwa ne dai ake sa ran gudanar da gwajin jirgin a karo na farko.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China