Jirgin kirar C919 wanda ke da adadin kujeru 158, zai iya yin tafiya mai nisan kilomita 4,075 a sararin samaniya, kuma kamfanin hada hadar jiragen saman fasinja na kasar Sin wato COMAC ne ya kera shi.
Ana sa ran fara gwajin farko na tashin jirgin na C919 ne a shekara mai zuwa, kuma za a yi gwajin jirgin har na tsawon shekaru 3 kafin shigar da shi kasuwa.
Kawo yanzu, kamfanin na COMAC, ya ce ya tantance bukatu 517 daga 'yan kasuwa masu sha'awar sayen jirgin su 21 a ciki da wajen kasar. (Ahmad Fagam)