in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana adawa da wata ayar doka dake da nasaba da harkar sojan Taiwan da Amurka ta sanya hannu
2017-12-14 20:12:29 cri
Mahukunan kasar Sin sun bayyana adawarsu da wata ayar doka mai alaka da harkar sojan Taiwan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai yau Alhamis, ya ce ayar dokar wadda Amurkar ta sanya cikin kasafin kudinta na shekarar 2018 , ta sabawa manufar "kasar Sin daya tak a duniya" da kuma manufofin sanarwar hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma, kuma hakan tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin.

Lu Kang ya ce, ko shakka babu kasar Sin ba ta goyon bayan wannan mataki, kuma tuni ta gabatar da kokenta ga gwamnatin Amurka.

A ranar Talata ce shugaba Trump ya sanya hannu kan wannan ayar doka, inda wasu sassanta suka amince sojojin ruwan Amurka da yankin Taiwan na kasar Sin su rika ziyartar juna.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China