in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bolar kayan latironi na haifar da babban kalubale ga muhalli da lafiyar bil'adama
2017-12-14 11:16:58 cri
Wani rahoton bincike mai taken "Global E-Waste Monitor 2017", ya nuna cewa, bolar kayayyakin laturoni da ake fitarwa a sassan duniya daban daban na matukar karuwa, lamarin da ke barazana ga lafiyar al'ummar duniya, baya ga illa da hakan ke da shi ga muhalli. Rahoton ya ce wannan matsala na kuma iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasashen duniya.

Kungiyar kasa da kasa ta harkokin sadarwa ITU, da jami'ar MDD ta UNU, da kuma kungiyar ISWA ne suka fitar da wannan rahoto, wanda a cikin sa aka bayyana cewa a shekarar 2016, yawan bolar kayan latironi kimanin tan miliyan 44.7 aka jibge a sassan kasashen duniya daban daban, adadin da ya haura na shekarar 2014 da kusan kaso 8 bisa dari. Har ila yau rahoton ya bayyana cewa, kaso 20 bisa dari ne kawai na wannan adadi aka sarrafa shi domin amfanin al'umma.

Tuni dai masana a wannan fanni suka yi hasashen karuwar adadin na shekarar 2016 da kaso kusan 17 bisa dari nan da shekarar 2021.

Da yake tsokaci game da hakan, babban sakataren kungiyar ITU Zhao Houlin, ya ce jibgewa, ko kone bolar laturoni, da ma rashin tsarin musamman na sarrafa wannan nau'i na bola, lamari ne dake bukatar matukar kulawa, musamman a wannan lokaci da ake ta samun karuwar amfani da kayayyakin latironi, kudurin da kuma ke cikin manufofin ci gaba na kungiyar ITU nan da shekarar 2020 mai zuwa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China