in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Faransa ya bukaci Netanyahu da ya rungumi damar wanzar da zaman lafiya
2017-12-11 10:49:37 cri

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya shawarci firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, da ya yi karfin halin rungumar matakan wanzar da zaman lafiya, ta yadda za a kai ga warware takaddamar da ta kunno kai tsakanin kasar sa da tsagin Falasdinu.

Mr. Marcron wanda ya yi wannan kira yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar tare, ya ce dakatar da gina sabbin matsugunan Yahudawa a birnin Tel Aviv, zai sanyaya rayukan Palasdinawa, ya kuma ba da dama warware ja in ja dake wanzuwa tsakanin sassan biyu.

A daya hannun kuma, shugaba Macron ya sake jaddada rashin amincewar sa da kudurin shugaban Amurka Donald Trump, na ayyana birnin Kudus a matsayin fadar mulkin kasar Isra'ila, yana mai cewa, hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa, don haka ba zai taba amincewa da matakin ba.

A nasa bangaren Mr. Netanyahu wanda ya gudanar da ziyarar aiki a kasar ta Faransa, ya ce zai ci gaba da shawarwarin wanzar da zaman lafiya da al'ummar Palasdinawa, muddin suka amince da kasancewar birnin Kudus a matsayin fadar mulkin Isra'ila.

An dai dakatar da shawarar wanzar da zaman lafiya da Amurka ke marawa baya tsakanin sassan biyu ne, tun cikin watan Afirilun shekarar 2014, bayan da sassan biyu da ba sa ga maciji da juna, suka gaza zuwa da wani sakamako mai gamsarwa, don gane da takaddamar su a fannin gina matsugunnai, da batun tsaro, da na shata kan iyakoki, da ma batun amincewa da matsayin kasar Palasdinawa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China