in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa za ta tura dakaru sama da dubu biyar zuwa yankin Sahel
2017-07-03 09:40:48 cri

A jiya Lahadi ne shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da takwarorinsa na kasashen yankin Sahel suka yi wata ganawa ta musamman a birnin Bamakon kasar Mali, a wani mataki na hada karfi da karfe don ganin bayan ayyaukan ta'addanci da ya gallabi yankin.

Kasashen yankin na Sahel ko G5 a takaice, da suka hada da Burkina-Faso, da Mali,da Mauritania, da Nijar da kuma Chadi sun kuma yanke shawarar kafa wata rundunar yaki da ayyukan ta'addanci ta hadin gwiwa, wadda kasar Faransa ta ce za ta ba da dakaru 5,250.

Aikin wannan runduna dai shi ne, yaki da ayyukan ta'addanci, da hana fataucin miyagun kwayoyi, da sace mutane, da taimakawa wajen ganin an dawo da doka da oda a wadannan kasashe, da dawo da mutanen da suka bar gidajensu da 'yan gudun hijira zuwa gida, da saukaka isar da kayayyakin agaji ga al'ummomin dake bukata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China