in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun nuna rashin amincewa da kudurin shugaban Amurka na mai da birnin Kudus hedkwatar mulkin Isra'ila
2017-12-07 12:31:59 cri

Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas, ya yi suka tare da watsi da matakin Amurka na mayar da birnin Kudus fadar mulkin kasar Isra'ila, yana mai cewa, yunkurin ya saba da kudure-kuduren kasashen duniya da dangantakar da ke tsakanin Amurka da Falasdinu.

Mahmoud Abbas ya ce matakin ba zai ba Isra'ila hallacin birnin ba, ya na mai cewa har abada kudus babban birnin ne ga Falasdin.

Ita ma Tarayyar Turai a jiya, ta yi bayyana damuwa matuka kan sanawar da Donald Trump ya yi ta mayar da birnin Kudus babban birnin Isra'ila.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, jami'ar dake kula da harkokin waje na Tarayyar Federica Mogherini ta ce, kungiyar na goyon bayan yarjejeniyar MDD ta kafa kasashen biyu, kuma matsayin abu ne da ba zai sauya ba.

Haka zalika shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce Faransa ba ta goyon bayan shawarar da shugaban Amurka ya yanke shi kadai, na daukar birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila. Emmanuel Macron ya ce, matakin na Amurka zai kara yamutsa al'amura a yankunan Falasdinu da Gabas ta Tsakiya.

A nasa bangaren, firaministan Isra'ila Benjemin Netanyahu, ya godewa shugaba Donald Trump bisa wannan muhimmin mataki da ya dauka.

Cikin sanarwar da ya fitar a daren Laraba bayan Trump ya kammala jawabinsa, Benjemin Netanyahu ya ce, sanawar ta Trump za ta taimaka wajen wanzar da zaman lafiya, inda ya ce, babu zaman lafiya matukar ba a dauki birnin Kudu a matsayin fadar mulkin Isra'ila ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China