in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta zartar da hukuncin kisa kan mutumin dake yiwa Isra'ila leken asiri
2017-10-25 10:27:36 cri

Abbas Jafari Dolatabadi, babban mai gabatar da kara a ma'aikatar shari'a ta kasar Iran ya ce, an yankewa wani mutum hukuncin kisa bisa zarginsa da yiwa hukumar leken asiri ta Mossad intelligence agency ta Isra'ila aiki.

Kamfanin dillancin labarai na ISNA ya rawaito Dolatabadi cewa, an yankewa mutumin hukuncin ne sakamakon zarginsa da hada kai da hukumar asiri ta Mossad.

Daya daga cikin laifukan da ake zargin mutumin shi ne, ya samar da wasu bayanai na sunayen wuraren ajiyar makaman nukiliyar kasar Iran 30, da kuma yin binciken ga jami'an Mossad game da yanayin karfin sojin kasar Iran, lamarin da ake ganin ya ba da damar yiwa wasu malaman kasar Iran din kisan gilla.

Dolatabadi ya ce, tuni wanda ake zargin ya amsa laifukan da ake tuhumarsa, kana ya nuna nadama game da irin rawar da ya taka wajen hallaka malaman kasar ta Iran.

Mutumin ya kuma bayyana cewa, ya sha gudanar da taruka da wasu jami'an Mossad su 8, kuma ya sanar da su wasu muhimman bayanai da suka shafi ayyukan dakarun sojin Iran, da kuma hukumar samar da makamashi ta kasar Iran.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China