in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar LREM ta shige gaba a zaben 'yan majalissun Faransa
2017-06-12 10:45:22 cri

Jam'iyyar LREM ta shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da jami'yyar MoDem dake kawance da ita, sun shige gaba a zagayen farko na zaben 'yan majalissun dokokin kasar da aka kada a ranar Lahadi.

Sakamakon sassan zaben da aka kada ya nuna cewa, jam'iyyar ta LREM ta lashe kaso 33.5 bisa dari na daukacin kuri'un da aka kada, inda ta sha gaban jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi ta conservatives, wadda ke da yawan kuri'un da ke tsakanin kaso 20.8 zuwa 22 bisa dari.

Jam'iyyar National Front mai fatan kafa kawancen 'yan adawa ta samu kaso 14 bisa dari, yayin da jam'iyya mai barin gado ta Socialist ke da kaso tsakanin 9 zuwa 10 bisa dari na daukacin kuri'un da aka kada.

Bisa jimillar sakamakon farko da aka tattara, ga alama LREM da kawayen ta, za su lashe kimanin kujerun wakilci 415 zuwa 455, cikin jimillar kujerun majalissar wakilan kasar 577, wanda hakan zai ba su karamin rinjaye kan gamayyar 'yan adawa.

Bisa hasashen da aka yiwa jaridar Le Figaro ta kasar, yawan kujerun wakilci da kawancen LERM za su samu za su kai tsakanin 400 zuwa 440.

A wani mataki na gwada farin jinin jam'iyyar da ya kafa kimanin shekara guda da ta gabata, shugaban Faransa mai ci Emmanuel Macron, ya ayyana sunan 'yan takarar jam'iyyar sa su 428 gabanin wannan zabe, ciki kuwa hadda 'yan takara mata 214, kuma kusan rabin su ba su taba rike wani mukami na gwamnati ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China