in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin: ya kamata bangarori daban daban su yi taka tsantsan kan batun matsayin birnin Kudus
2017-12-06 20:07:32 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana yau Laraba a birnin Beijing cewa, batun matsayin birnin Kudus na da sarkakiya. Don haka ya kamata bangarori daban daban su dora muhimmanci kan zaman lafiya, da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya, su kuma yi taka tsantsan, don kaucewa dagula tushen warware batun Palesdinu, wanda tuni ake kokari a kansa tsawon lokaci. Kana ya ce ya dace a dauki matakai na magance barkewar sabon rikici a yankin.

Ban da wannan kuma, Geng Shuang ya ce a ko da yaushe, kasar Sin na tsayawa tsayin daka, kan ci gaban yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, da mara wa jama'ar Pelesdinu baya wajen samun hakkinsu bisa doka, tare da goyon bayan kafuwar kasar Palesdinu mai cikakken 'yanci, wadda aka amince da shata iyakarta da tsagin Isra'ila tun a shekara 1967, tare da batun mai da birnin Kudus ta Gabas a matsayin hedkwatar mulkinta.

Haka zakila, kasar Sin ta yi kira da a dukufa kan warware sabani ta hanyar shawarwari a karkashin inuwar kudurorin MDD da abin ya shafa, a kokarin shimfida zaman lafiya da na karko a yankin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China