in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashin hankali a Sudan ta kudu ya hallaka mutane 45
2017-12-09 12:23:09 cri

A kalla mutane 45 ne suka rasa rayukan su, baya ga wasu 31 da suka jikkata, yayin wani dauki ba dadi da sassa biyu na 'yan kabilar Dinka suka gwabza a yankin tsakiyar Sudan ta kudu.

Ministan watsa labarai na jihar Western Lakes Shadrack Bol Machok, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, fada ya barke tsakanin tsagin haular Rup da na Pakam tun a ranar Laraba, a yankin Nap mai nisan kilomita 80 daga birnin Rumbek fadar mulkin jihar.

Mr. Machok ya ce, duk da shawarwari da aka sha yi a baya tsakanin sassan biyu, 'yan haular Rup wadanda Pakam suka kora daga gundumar Malek, biyowa bayan rikicin shekarar 2014 sun yi yunkurin daukar fansa, tare da kwato filayen noma da suka yi ikirarin an kwace masu, lamarin da shi ne ya haifar da tashin hankalin na baya bayan nan.

Jami'in ya kuma kara da cewa, tuni mahukunta suka fara shirin karbe makamai daga hannun fararen hula, biyowa bayan umarnin hakan da gwamnatin kasar ta bayar tun a ranar 27 ga watan Yuni. Ya ce an shirya daukar wannan mataki ne dai da nufin dakile amfani da makamai, a duk lokacin da rashin jituwa ya auku tsakanin fararen hula.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China