Sanarwar ta ce, ana iya gano boma-bomai da matsakaicin yawansu ya kai 150 a ko wane wata a kasar. Wadannan boma-bomai ba kawai sun hana fararen hula tserewa daga yankunan da ake fama da rikici ba, har ma sun kawo cikas ga taimakon jin kai, tare kuma da hana ci gaban tattalin arziki da al'ummar kasar baki daya.
Baya ga haka, sanarwar ta ce, ofishin na kokarin aikin bincike da kawar da boma-boman sakamakon yaki da kasar ta Sudan ta kudu ta fuskanta, da nufin ba da tabbacin tsaro ga masu aikin kiyaye zaman lafiya, kana da samar da yanayi mai kyau wajen gudanar da taimakon jin kai da farfado da yanayin zamantakewar rayuwar yau da kullum na 'yan kasar. (Bilkisu)