in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Sudan ta Kudu sun amince da tura dakaru zuwa yankunan da ba a yiwa shinge ba
2017-11-01 13:07:56 cri
Mahukuntan kasashen Sudan da Sudan ta kudu, sun amince da su tura sojojin su sassan kan iyakokin kasashen biyu, inda ba a sanyawa dokar hana jibge sojoji ba domin tabbatar da tsaro.

Kasashen biyu dai sun amince da hakan ne a jiya Talata, yayin taron hadin gwiwa na shirin siyasa da tsaron kasashen biyu, wanda ya gudana a birnin Khartoum.

Ministan tsaron kasar Sudan Awad Ibn Auf, da takwaransa na Sudan ta kudu Kuol Manyang Juuk ne suka sanya hannu a madadin kasashen biyu, kan takardar yarjejeniyar da ta tanaji wannan kuduri.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin rundunar sojojin kasar Sudan, Ahmed Khalifa Al-Shami, ya ce kasashen biyu sun amince su sake farfado da hukumar hadin gwiwa ta inganta tsaro da siyasa, tare da tabbatar da nasarar tantance kan iyakokin kasashen biyu.

Al-Shami ya kara da cewa, sassan biyu sun amince da gaggauta aiwatar da wannan manufa cikin kasa da watanni 6, yayin da ake sa ran hukumar tsaro da siyasar kasashen za ta yi taro a birnin Juba, fadar mulkin Sudan ta kudu a watan Janairun shekarar 2018, domin nazartar ayyukan da aka sanya gaba.

Tuni dai hukumar ta dukufa wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki, gabanin ziyarar da shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit zai kai birnin Khartoum a yau Laraba.

Batun shata kan iyakoki dai na cikin manya kalubale da ke dakile aniyar kasashen biyu game da warware sabani. Sassan da suka fi jawo takaddama dai sun hada da yankin Abyei mai arzikin mai, da Mile 14, da Dabatal-Fakhar, da Jabel Al-Migainis, da Samaha, da kuma Kafia Kanji. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China