Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan cikin sakon taya murna da ya aikawa dandalin kare hakkin bil-Adam na kasashe masu tasowa da aka bude a yau a nan birnin Beijing, ya kuma mika sakonsa na fatan alheri ga dandalin, wanda ake fatan zai mayar da hankali kan yadda ake yayata batun kare hakkin bin-Adam a kasashe masu tasowa da ma duniya baki daya.
Ya ce wajibi ne, a yayata batun kare hakkin dan-Adam bisa la'akari da yanayi da bukatun al'ummomin kasashen da batun ya shafa.(Ibrahim)