Ministan harkokin waje na kasar Sin Mr. Wang Yi, ya ce kasar Sin ta samu ci gaba na a zo a gani, tare kuma da cimma gaggarumar nasara ta fannin kare hakkin bil Adam, a karkashin jam'iyyar Kwaminis ta kasar tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, kuma dalili shi ne yadda ta tsaya tsayin daka a kan bin hanyar da ke da sigar musamman ta kasar.
Ministan ya fadi haka ne, a lokacin da ya gabatar da jawabi a gun taron dandalin tattaunawa game da kare hakkin bil Adam a tsakanin kasashe maso tasowa karo na farko, wanda aka bude yau Alhamis a nan birnin Beijing.(Lubabatu)