in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: Sin na sa kaimi ga ginin duniya mai cike da daidaito
2017-12-01 09:11:58 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce manufar kasar sa game da harkokin diflomasiyya, ita ce mara baya ga samar da daidaito da cin moriya tare tsakanin daukacin kasashen duniya.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin taron dandalin tsoffin shugabannin wasu kasashen duniya, da masana, tare da 'yan kasuwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin.

Ya ce sabon salon diflomasiyyar Sin na kunshe da inganta alakar kasashen duniya cikin girmamawa, da adalci, tare da cin gajiya tare. Kaza lika hakan ya kunshi kaucewa daukar doka a hannu, da hawa teburin shawarwari, da kaucewa fito na fito, tare da bunkasa hadin gwiwa.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar sa za ta ci gaba da bin tsarin zaman lafiya wajen samar da ci gaba, kasancewar tun fil azal, Sin ba ta taba tsoma baki cikin harkokin wata kasa ba, karkashin mu'amalar diflomasiyya.

Kaza lika shugaban na Sin ya ce, Sin ba za ta taba aiwatar da manufar mulkin mulaka'u kan wata kasa ba, kamar yadda ake gani wasu manyan kasashen duniya na yi.

Bugu da kari Sin za ta zage damtse wajen bada gudummawa ga wanzuwar managarcin shugabanci a duniya, ciki hadda tallafawa wajen warware sabani tsakanin kasashe, da shiga a dama da ita a ayyukan wanzar da zaman lafiya, da tabbatar da an aiwatar da yarjejeniyar Paris, da ma kudurorin dake kunshe cikin muradun samar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China