in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An mai da hankali kan aikin kau da talauci a taron fasahar yanar gizo ta Internet
2017-12-04 20:02:09 cri
A ranar Litinin din nan aka gudanar da wani dandalin tattaunawa mai taken "Cimma Moriya tare: Kau da talauci da yanar gizo ko Internet", a gabar taron fasahar yanar gizo ta Internet na kasa da kasa karo na 4, wanda ke gudanar a garin Wuzhen dake gabashin kasar Sin.

Mahalarta dandalin sun hada da wakilan hukumar abinci da aikin gona ta MDD (FAO), da na hukumar kula da harkokin mata ta Majalisar, da hadaddiyar kungiyar aikin sadarwa ta kasa da kasa, da asusun bada lamuni na duniya (IMF). Sauran sun hada da bankin duniya, da na wasu gwamnatoci da hukumoni na kasashen Amurka, da Ghana, da Habasha, da dai sauransu. Sai kuma wasu sanannun 'yan kasuwa, gami da wakilan jama'ar wasu wuraren dake fama da talauci mai tsanani dake kasar Sin.

A yayin dandalin da aka kira, an mai da hankali kan ajandar samar da ci gaba mai dorewa na shekarar 2030 wanda MDD ta gabatar, da musayar ra'ayi kan dabarun da ake amfani da su wajen rage talauci, ta hanyar fasahar yanar gizo ta Internet.

Sa'an nan kamfanofi masu alaka da fasahar zamani ta yanar gizo, su ma sun yi alkawarin kulla hulda tare da wasu wurare masu fama da talauci, ta yadda za a rika taimaka musu a nan gaba.

Haka zalika, a wajen taron, wakilan gwamnatocin wasu kasashe, da wasu manyan 'yan kasuwa sun yaba wa matakan da kasar Sin ta dauka a fannin yaki da talauci, inda suka ce matakan sun zama abin koyi ga sauran kasashe. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China