in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoton nazarin tattalin arzikin Zambia ya nuna nagartattun manufofin gwamnatin kasar
2017-08-28 10:53:14 cri

Ministan kudin kasar Zambia Felix Mutati, ya ce rahoton nazarin tattalin arzikin kasar da ya nuna ci gaban da kasar ta samu, na alamta managartan dabarun da gwamnatin kasar ta aiwatar.

Felix Mutati, ya ce an samu ci gaban ne biyo bayan muhimman sauye-sauye da kasar ta dauka karkashin tsayayyen tsarin tattalin arziki da raya kasa, ta hanyar aiwatar da dabarun amfani da kudaden shiga da janye tallafin da sake fasalin bangaren makamashi da baza komar tattalin arziki ta hanyar raya bangarorin noma da na masana'antu.

Sakamakon nazarin da hukumar tantance tattalin arzikin kasar ta fitar, abu ne da zai ja hankalin masu zuba jari, domin zai ba su tabbacin cewa, kasar na kan tafarkin samun ci gaba da tsarin tattalin arziki mai dorewa.

Hukumar nazarin arzikin kasa ta duniya ta sake bitar darajar takardar kudin kasar, inda ta sanyata a matakin daidaito daga matakin koma baya.

Ta kuma alakanta sakamakon bitar da raguwar gibin tsakanin kudaden da gwamnati ke kashewa da kudaden shigarta da kuma tarin basussuka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China