in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambia ta jinjinawa gudummawar Sin a fannin bunkasa ilimi
2015-08-21 09:42:36 cri

Mahukuntan kasar Zambia sun jinjinawa kasar Sin bisa tallafin da take samarwa a fannin bunkasar ilimi tsakanin al'ummar kasar.

Mataimakin ministan ilimin kimiyya da koyar da sana'o'i na kasar, Sydney Mushanga ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin bikin ban kwana da wasu daliban kasar, wadanda suka samu guraben karatu a jami'o'in kasar Sin a bana.

Mushanga ya kara da cewa, guraben karatu da Sin ke samarwa daliban kasar Zambia, na taimakawa ci gaban dangantakar kasashen biyu, baya ga daga matsayin Zambia ta hanyar samar da karin kwararru.

Daga nan sai ya bukaci daliban da su mai da hankali kan karatunsu, su kuma kauracewa shiga hanyoyin da ka iya gurgunta damar da suka samu.

A nasa bangare, Mr Pan Qingjiang, jami'in a ofishin jakadancin Sin dake kasar ta Zambia, cewa ya yi, Sin ta yanke shawarar kara yawan guraben karatu ga daliban kasar zuwa 49 a bana, duba da irin sha'awar karatu a Sin da daliban kasar ta Zambia ke dada nunawa.

Ya ce, hakan ya shaida kyakkyawar dangantakar dake akwai tsakanin al'ummar Sin da na Zambia, da kuma babbar dama ta musaya da hadin gwiwa a fannin ilimi dake akwai tsakanin kasashen biyu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China