Gwamnatin kasar Zambia ta musanta zargin da aka yi mata, na baiwa wani jami'in asusun ba da lamuni na IMF na goro, domin ya tallafa mata samun taimako da take nema daga asusun.
Wasu kafofin watsa labarai na yanar gizo dai sun zargi gwamnatin shugaba Edgar Lungu, da baiwa shugaban tawagar IMF Tsidi Tsikata tosiyar baki, yayin ziyarar da ya kai kasar a watan da ya gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa, Mr. Tsikata ya gana da shugaba Lungu a yayin ziyarar ta sa, inda suka tattauna game da yiwuwar baiwa kasar ta Zambia damar cin moriyar taimako daga tanajin bashi mai dogon zango da IMF din ke baiwa wasu kasashe.(Saminu)