in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar adawa a Zambia ta ce ba za ta shiga babban zaben kasar ba
2016-05-18 09:32:00 cri

Jam'iyyar adawa a kasar Zambia ta bayyana cewa, ba za ta shiga babban zaben kasar da ake shirin gudanarwa a wannan shekara ba, bisa abin da kira da mulkin danniya da gwamnati mai ci a kasar ke yi.

Jagoran 'yan adawar, kana mutumin da ya zo na shida a zaben shugabancin kasar na shekarar da ta gabata Eric-Chanda ya ce, gwamnati ba ta baiwa 'yan adawa damar bayyana ra'ayoyinsu, don haka, jam'iyyarsu ta yanke shawarar kauracewa babban zaben kasar da zai gudana a ranar 11 ga watan Agustan wannan shekara.

Ya ce, tun lokacin da aka kama shi bisa zargin batawa shugaba Edgar Lungu suna yake zuwa kotu, maimakon ya mayar da hankali wajen yakin neman zabe. Sannan kotun ba ta ba shi damar ya je yakin neman zabe gabanin manyan zabukan kasar da ke tafe.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China