An bude taron kungiyar matan Afrika karo na farko a birnin Marrakech na Morocco.
Taron mai taken "samar da shugabanci na gari tare da matan Afrika" ya ja hankalin manyan 'yan kasuwa 300 daga kasashe 37, galibinsu na Afrika.
Taron na da nufin bayyana muhimmancin shugabancin mata a kasashen Afrika da karfafawa kamfanonin Afrika da na kasashen ketare gwiwar marawa mata baya.
Yayin taron na yini uku, mahalarta za su samu damar tattauna muhimman batutuwa da nufin ba mata karin damammakin ciyar da kasashensu gaba.
Za a gudanar da taruka da tattaunawar hadin gwiwa da masana daga kasashen ketare domin muhawara kan batutuwa daban-daban da suka hada da harkokin gona da makamashi da kasuwanci da na kudi da ruwa da kuma abinci mai gina jiki. (Fa'iza Mustapha)