in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kolin Morocco ya share fagen inganta shugabancin mata
2017-09-28 13:31:49 cri

Taron dandalin matan Afrika da aka gudanar a karon farko a birnin Marrakech na kasar Morocco, ya samar da wani tsari wanda zai inganta sha'anin shugabanci ga mata.

Bangarori shida ne taron ya cimma matsaya kansu, da suka hada da bangaren aikin gona, makamashi, sana'o'in hannu, bangaren kudi, abinci mai gina jiki, da kuma samar da ruwa.

Yayin taron da aka kaddamar, an bukaci mata 'yan kasuwa na kasashen Afrika su shiga cikin shirin ci gaba wanda aka kebe kudi sama da Euro miliyan 5 don samarwa matan Afrika damammaki, ta yadda za su ciyar da kasashensu gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China