in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kebe daa biliyan 7.5 domin kare muhalli
2017-11-24 09:43:50 cri
Ma'aikatar kare muhalli ta kasar Sin ta bayyana cewa, gwamnati ta kebe zunzurutun kudi har RMB biliyan 49.7, kwatankwacin dala biliyan 7.5 domin gudanar da ayyukan kare muhalli a wannan shekara.

Jami'i a sashen harkokin kudi da tsare-tsare a ma'aikatar You Yanxin, ya shaidawa taron manema labarai cewa, ya zuwa yanzu an fitar da Yuan biliyan 39 domin aikin kare gurbatar iska, ruwa da kuma kasa.

A cewar You, an kuma kebe Yuan biliyan 16 cikin wannan adadi domin ayyukan kare gurbatar iska a matakan larduna na yankuna 13 da suka hada da Beijing-Tianjia-Hebei da kuma yankunan da ke makwabta da su, da yankin kogin Yangtze da na kogin Delta.

Ya ce, tun lokacin da aka fara aiwatar da shirin raya kasa na 13 daga shekarar 2016-2020, yawan kudaden da gwamnatin tsakiya ta ke kashewa kan wannan aiki ya kai Yuan biliyan 27.2, matakin da ya taka muhimmiyar rawa waje kara ingancin iska a muhimman yankuna.

Haka kuma gwamnatin tsakiyar kasar ta Sin ta kebe Yuan biliyan 8.5 domin kare gurbatar ruwa, baya ga Yuan biliyan 6.5 da aka ware a fannin kare gurbatar kasa ko filaye.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China