in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka sun alkawarta maida wadanda suka makale a Libya kasashen su
2017-12-01 10:59:46 cri
Wakilan kungiyar tarayyar Turai ta EU da na kungiyar hadin kan Afirka ta AU, sun alkawarta daukar dukkanin matakan da suka wajaba, na ganin sun dakile kwararar baki 'yan ci rani zuwa Turai ba bisa ka'ida ba.

A jiya Alhamis, Wakilan sassan biyu dake taro karo na 5 a birnin Abidjan, cibiyar kasuwancin kasar Cote d'Ivoire, sun kuduri aniyar mayar da 'yan ci ranin Afirka da suka makale a kasar Libiya zuwa kasashen su na asali.

Da yake tsokaci game da hakan, shugaban kasar Guinea Alpha Conde, ya ce mahalarta taron tsagin nahiyar Afirka sun kuma amince da kafa rundunonin yaki da safarar bil'adama.

Shugaba Conde, wanda kuma shi ne shugaban karba karba na kungiyar AU na wannan karo, ya kara da kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki, da su tabbatar da hukunta masu hannu a aikata laifukan da suka jibanci keta zarafin bil'adama.

A ranar Laraba ne dai kasashe 9 dake halartar taron hadin gwiwar EU da AU, suka amince da daukar matakan gaggawa na kwashe baki 'yan ci rani wadanda suka makale a kasar Libiya zuwa kasashen su na ainihi.

Duk da cewa taken taro shi ne "zuba jari a fannin matasa domin samar da ci gaba mai dorewa," batun bakin haure, da kalubalen ayyukan ta'addanci ne ya mamaye tattaunawar ta yini biyu, musamman a gabar da Turai ke yunkurin dakile kwararar bakin haure, da shawo kan matsalar hare haren ta'addanci dake addabar wasu kasashen nahiyar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China