in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakada: Kasar Sin na goyon bayan Afrika a kokarinta na raya masana'antu
2017-11-21 12:35:11 cri
Zhou Pingjian, jakadan kasar Sin dake Najeriya ya bayyana cewa, kasarsa na goyon bayan nahiyar Afrika kan shirinta na raya masana'antu, jakadan ya bayyana hakan ne a Abuja, fadar mulkin Najeriyar.

Da yake jawabi a wajen taron bikin tunawa da ranar masana'antu ta Afrika, wanda aka kebe 20 ga watan Nuwambar kowace shekara, kuma an fara wannan bikin ne tun a shekarar 1990, Zhou yace, bangaren masana'antu yana da matukar muhimmanci wajen bunkasa cigaban Afrika.

Jakadan ya shedawa mahalarta taron cewa, akwai bukatar samar da wasu muhimman tsare tsare wadanda zasu tabbatar da samar da kyakkyawan yanayin masana'antu a nahiyar.

Yace aiwatar da tsarin kasuwanci mai 'yanci a tsakanin nahiyoyi yana da matukar muhimmanci, yace amma idan ba'a inganta sha'anin masana'antu ba, nahiyar zata tsaya ne kawai wajen sayar da kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa, daga karshe kuma ta dinga sayo kayayyakin da aka sarrafa din daga kasashen ketare.

Yace yana da matukar muhimmanci ga nahiyar Afrika ta dinga samar da kayayyakin da ake bukatar amfani dasu a cikin gida harma ta dinga fitar dasu kakashen ketare, domin ta samu damar ciyar da alummarta, kana ta kuma samu kudaden shiga daga kasashen ketare.

Tun da farko, ministan ciniki masana'antu da zuba jari na Najeriyar, Okechukwu Enelemah, ya nanata bukatar dake akwai ga Afrika wajen tabbatar da bunkasa cigaban masana'antu domin kaucewa dogaro kacokan kan kasashen duniya mafiya karfin masana'antu wajen sayen kayayyakin bukatun yau da kullum.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China