Mataimakin shugaban hukumar CCPIT Chen Zhou, ya ce baje kolin na hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Afrika domin inganta ayyukan masana'antu da hukumar CCPIT ta shirya, zai gudana ne a Nairobin kasar Kenya daga ranar 13 zuwa 16 ga watan Decemba.
Chen Zhou ya ce an kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da baje kolin da CCPIT ta shirya a nahiyar Afrika a karon farko.
Ya ce jimilar kamfanonin kasar Sin 56 ne za su shiga baje kolin inda za su nuna kayayyaki masu matukar inganci da fasahar zamani wajen sarrafa amfanin gona da manyan Injina da na shimfida layin dogo da ginin titi, da samar da hanyoyin sadarwa.
Ya kara da cewa, yayin da Afrika ke da arzikin albarkatu da jama'a, kuma take kan matakin fara raya bangaren masana'antu, kasar Sin na da fasaha da injina da kwarewa da kuma kudin da za ta taimakawa nahiyar cimma burinta na samun ci gaba mai dorewa ta hanyar dogaro da kanta. (Fa'iza Mustapha)