Sakatare Janar na Kungiyar ma'aikatan jinya ta kasar Seth Panyako, ya ce za a fara aiwatar da kunshin yarjejeniyar da aka cimma cikin kwanaki 30, ya na mai bukatar ma'aikatan su koma bakin aiki daga yau Juma'a.
Tun a watan Yunin da ya gabata ne ma'aikatan jinyar suka kauracewa wuraren aiki, saboda a cewarsu, an saba yarjejeniyar da suka cimma da Gwamnati. (Fa'iza Mustapha)