in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarayyar Turai da Afirka na duban hanyoyin zuba jari a harkar matasa
2017-11-29 10:24:59 cri

Gabanin taron hadin gwiwar kungiyar tarayyar Turai ta EU, da takwararta ta Afirka AU da za a bude yau Laraba a kasar Cote d'Ivoire, masharhanta na ci gaba da tsokaci game da bukatar zuba jari a harkokin matasan Afirka, domin cin gajiyar albarkatun al'umma da nahiyar ke da su.

Game da hakan, shugabar ofishin harkokin waje ta kungiyar EU Federica Mogherini, ta ce taken taron na wannan karo shi ne "zuba jari a harkokin matasa domin samar da ci gaba mai dorewa". Ta ce, taron wanda shi ne irin sa na 5 da za a gudanar, a wannan karo zai sanya sha'anin matasa a sahun gaba a karon farko a tarihi.

A wani ci gaban kuma, yayin taron dandalin bunkasa harkokin kasuwanci na kungiyar ta EU da kasashen Afirka, kwamishinan sashen hadin gwiwar kasa da kasa, da samar da ci gaba a hukumar gudanarwar EUn Neven Mimica, ya ce inganta yanayin zuba jari a nahiyar Afirka na da matukar muhimmanci a fannin samar da guraben ayyukan yi ga matasan Afirka, kaza lika hakan zai tabbatar da ci gaba mai dorewa a nahiyar.

Masu fashin baki dai na da mabanbantan ra'ayoyi game da batun zuba jari a Afirka. Wasu dai na ganin baiken manufar datse tallafin da EUn ke baiwa wasu kasashen Afirka musamman ma masu karamin karfi, tallafin da ke taka muhimmiyar rawa, wajen raya kasashen da ba sa iya jawowa kan su jarin waje cikin sauki.

Da yake tsokaci game da hakan, masanin tarihi a jami'ar Felix Houphouet Boigny dake birnin Abidjan farfesa Bamba Abdoulaye, ya ce kasashen Turai ba za su zuba jarin a zo a gani a harkokin matasan nahiyar Afirka ba, suna dai da burin bayyanawa shugabannin nahiyar bukatar yin hakan ne kawai.

Farfesa Abdoulaye ya kwatanta tarukan da kungiyar ta EU ke yi da kasashen nahiyar Afirka, da wanda kasashen na Afirka ke gudanarwa da kasar Sin, yana mai cewa, na Turai zance ne kawai na fatar baki, yayin da Sin ke da niyyar gudanar da alkawuran ta a aikace.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China