in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Venezuela ta soki sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba mata
2017-08-26 13:07:44 cri

Ministan harkokin wajen Venezuela Jorge Arreaza, ya bayyana sabbin takunkuman tattalin arziki da Amurka ta kakabawa kasarsa da barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi na amfani da karfin soji a kasar dake Kudancin Amurka, a matsayin abu maras ma'ana da mugunta a kan kasar dake zaman lafiya.

Jorge Arreaza ya bayyana haka ne a jiya Jumma'a, yayin ganawarsa da Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres a hedkwatar majalisar dake New York, inda kakakinsa ya ce tattaunawar tasu ta maida hankali ne kan halin da kasar ke ciki.

Bayan shafe watanni ana fama da rikici da zanga-zangar kin jinin Gwamnati a Caracas, an zabi sabuwar majalisar da za ta samar da sabon kudin tsarin mulkin kasar, wanda zai maye gurbin majalisar dokoki dake karkashin ikon bangaren adawa, al'amarin da ya sa Washington kakaba mata takunkumi.

Kakakin ya ce Sakatare Janar na MDD ya jaddada matsayinsa inda ya bayyana samun maslahar siyasa bisa tattaunawa da cimma yarjejeniya tsakanin Gwamnati da masu adawa da ita, a matsayin muhimmin wajen gaggawar magance kalubalen da wata kasa ke fuskanta, bisa martaba dokokin kasar da hakkin dan adam. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China