in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya da EU sun tattauna game da tsaron kan iyaka
2017-11-27 10:16:17 cri

Gwamnatin kasar Libya tsagin da MDD ke marawa baya, da jami'an shirin tarayyar Turai EU mai tallafawa kare kan iyakokin kasar ko EUBAM a takaice, sun tattauna game da matakan kare kan iyakokin kasar ta Libya.

Wata sanarwa da ofishin watsa labarai na firaministan kasar Fayez Mustafa al-Serraj ya fitar, ta ce sassan biyu sun yi doguwar tattaunawa da nufin zakulo dabaru mafiya dacewa, na shawo kan kwararar 'yan ta'adda, da bakin haure ba bisa ka'ida ba ta sassan iyakokin kasar Libya.

Sanarwar ta rawaito firaminista Al-Serraj na cewa, iyakokin kasar Libya na da matukar tasiri, musamman idan aka yi duba da kalubalen ayyukan ta'addancin da ake fuskanta, da na kwararar bakin haure da masu fataucin bil'adama da kasar ke fama da shi.

Ya ce, akwai matukar bukatar hadin gwiwa tsakanin kasar Libya da tawagar tarayyar Turai, domin cimma burin da aka sanya gaba na dakile wadannan matsaloli.

Sanarwar ta bayyana bukatar daukar kwararan matakai game da tsaron kan iyakoki, da ma warware matsalolin siyasa dake raunana karfin gwamnatin kasar na fuskantar kalubale.

A wani ci gaban kuma, a 'yan kwanakin baya ne jakadar kungiyar tarayyar ta Turai a Libya Bettina Muscheidt ta gana da Mr. Serraj, inda kuma ta bayyana burin shirin EUBAM, na sake maido da ayyukan sa birnin Tripoli, fadar mulkin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China