in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran za a shigar da wasannin kwamfuta a wasannin Olympics na shekarar 2024
2017-11-15 17:46:47 cri

A kwanakin baya, kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya wato IOC, ya sanar da cewa, an tabbatar da wasannin kwamfuta wato Esport, a matsayin irin wasanni da za a rika gudanarwa a hukunci a gasar ta Olympics. Don haka, kwamitin IOC na shirin shigar da gasar dake tafe a shekara ta 2024.

Idan aka shirya tsarin gasar yadda ya kamata, ana sa ran cewa, za a ga irin wadannan wasanni a gasar Olympics din ta 2024 da za a gudanar a birnin Paris na kasar Faransa.

A shekarun baya baya nan, an gudanar da wasannin kwamfuta a manyan filayan wasa na kasa da kasa. A shekarar 2016, an gudanar da gasar wasannin kwamfuta a filin wasa na Madison Square Garden dake birnin New York har tsawon dare biyu, an kuma sayar da dukkan tikitin gasar. Kwamitin IOC yana fatan masu kallo za su ci gaba da mai da hankalinsu kan wasannin Olympics a halin yanzu, shi yasa ake kuma canja tsarin wasannin dake cikin sa.

Kaza lika kasashen Sin kasar Japan, suna baya idan an kwatanta da kasashen Turai da Amurka a fannin yawan lambobin yabo da ake samu a wasannin Olympics, a nan ma kwamitin IOC na kara jawo hankalin masu kallo na nahiyar Asiya, hakan ne kuma ya sa ya kamata ya yi kokarin shigar da wasannin kwamfuta a gasar wasannin Olympics.

Babu shakka, ana bukatar doguwar hanya wajen shigar da irin wadannan wasanni a cikin wasannin Olympics. Na farko, ya kamata kwamitin IOC da masu kallo su san yanayin wasanni, da kuma yadda ake horar da 'yan wasa da inganta fasahohinsu. Na biyu, shugaban kwamitin IOC Thomas Bach, ya warware matsalar kasancewar mafiya yawan wasannin kwanfuta na tattare da nuna karfin tuwo ko keta. A karshe dai, ana bukatar da kafa wata hukumar hadin gwiwa kamar FIFA, don tabbatar da bin ka'idojin kwamitin IOC a wannan fanni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China